Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya ƙi mayar da kuɗin da aka tura cikin asusun bankin sa bisa kuskure, zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru biyar zuwa 10 a gidan gyaran hali.
CBN bayyana cewa riƙe kuɗin da aka tura wa mutum bisa kuskure maimakon a maida wa mai kuɗin abin sa, laifi ne da doka ta tanadi hukunci a kan sa. Daga nan bankin ya buƙaci ’yan Nijeriya da su mayar da duk kuɗin da aka tura musu bisa kuskure ga masu haƙƙin mallakar su.
Wannan kakkausan gargaɗi dai ya fito ne daga bakin Daraktar Sashen Kula da Abokan Hulɗa da kuma Hukumomi ta CBN, Hakama Sidi-Ali.
Ta yi wannan gargaɗi a ranar Alhamis, yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka shirya ƙarƙashin shirin bankin mai suna CBN Listens Programme, wanda aka gudanar a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Yayin da ake ƙara samun faɗaɗar hadahadar kuɗi ta hanyoyin sadarwa na zamani, a waje ɗaya kuma masu tura kuɗaɗe ta hanyoyin tura kuɗi cikin gaggawa, musamman ATM, PoS da kuma ta wayar hannu kan fuskanci tura kuɗi zuwa wani asusu daban a bisa kuskure.
Inda matsalar ta fi tsananta kuma ita ce idan wanda aka tura wa kuɗin bisa kuskure ya ƙi maida wa mai kuɗin abin sa.
Wannan dai shiri ne da aka bijiro da shi domin jin ra’ayoyin jama’a, karɓar ƙorafe-ƙorafen su dangane da matsalolin da suka fuskanta ko suke fuskanta a tsarin hadahadar kuɗi a banki. Kuma a ƙarƙashin shirin, CBN na karɓar shawarwari daga masu ruwa da tsaki da kuma jama’a.
Dangane da batun ƙorafe-ƙorafe kuwa, Hakama ta ce idan bankin da aka kai wa ƙara ko ƙorafi ya gaza tabbatar da karɓar ƙorafin cikin kwanaki uku, bayar da lambar bibiyar ƙorafin, ko warware matsalar cikin wa’adin da dokar kare abokan ciniki ta tanada, abokin cinikin na iya kai ƙarar zuwa ga Daraktan Sashen Kare Abokan Ciniki da Haɗa su da Tsarin Kuɗi (CPFD) na CBN.
Dalilin kafa shirin ‘CBN Listens’
A cikin jawabin na ta, Hakama ta bayyana cewa an ƙirƙiri shirin ‘CBN Listens’ ne domin ƙarfafa hulɗa tsakanin bankin da masu ruwa da tsaki, tare da inganta tsara manufofi ta hanyar karɓar ra’ayoyi da shawarwari daga mutane, ‘yan kasuwa da cibiyoyin hada-hadar kuɗi.
Ta ce shirin ya nuna imanin bankin cewa aiwatar da manufofi yadda ya kamata yana buƙatar tattaunawa akai-akai da fahimtar juna tsakanin masu tsara dokoki da kuma al’ummar da ake yi wa hidima.




